Wata kotu ta yankewa wani matashi hukuncin kisa bisa kamashi da laifin fashi da makami a jihar Oyo

0 80

Wata babbar kotu dake Zamanta a Ibadan babban birnin jihar Oyo ta yankewa wani matashi mai suna Oriyomi Felix dan shekara 35 hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta kamashi da laifin fashi da makami.

Kotin ta kama matashi ne da laifuka biyu, da suka hada da fashi da makami da kuma yin sojan gona.

Alkalin kotun kuma mai shariah Bayo Taiwo ne ya yanke wannan hukuncin a yau Litinin, ya kuma ce mai gabatar da karar Mrs Sandra Stella ta gabatar da dukkanin hujjojin da suka tabbatar da cewa wanda ake zargin ya aikata laifukan.

Mai shariar ya kuma ce wanda ake zargin da abokanan sa masu suna Kamorudeen Adeyemi, Ibrahim Sariyu, Alhaji Alowonle Nurudeen an same su da lafin fashi da makamin da suka aikata a ranar 12 ga watan Disamaba na 2017 a unguwar Tose Moniya Zone II dake Ibadan dauke da bindigogi.

Anata bangaren mataimakiyar daraktan ma’aikatan shariah ta jihar Stella, tace wadanda ake zargin sun shiga gidan wanda akayiwa fashin ne dauke da bindigogi kuma suka sace masa Laptop, Wayoyi da kuma wasu sarkuna daban daban.

Leave a Reply

%d bloggers like this: