Wasu waɗanda ba sa bin addini a Kenya na taimaka wa mutane da kuɗin jinya da kuma ɗaukar nauyin jana’izar ‘yan uwansu da zimmar raba su da addinansu.

Ƙungiyar mai suna Atheists In Kenya Society (AIK) ta fuskanci koma-baya lokacin da sakatarenta na ƙasa ya bar muƙaminsa kuma ya koma addinin Kirista.

Yanzu ƙungiyar na roƙon duk wanda “ba ya bin addini, wanda bai damu da addini ba, wanda bai yarda da samuwar Allah ba” da ya je shafinta ya biya wasu kuɗi don yin rajista don ya samu tallafin asibiti.

Fiye da kashi 97 cikin 100 na ‘yan Kenya na bin addini, a cewar binciken cibiyar Pew Research.

Asalin Rahoton: BBCHausa

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: