Gwamnatin tarayya baza tayi kasa a gwiwa ba wajen cigaba da yakar yan ta’adda -Osinbajo

0 99

Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo yace gwamnatin tarayya baza tayi kasa a gwiwa ba wajen cigaba da yakar ‘yan ta’adda da masu tayar da zaune tsaye.

Mataimakin shugaban kasar ya sanar da haka a jiya a wajen taron lakca na tunawa da shugabancin Sir Ahmadu Bello na bana, wacce Sarkin Lafia, Mai Shari’ah Sidi Bage, ya gabatar a Kano.

Gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Kano ne suka shirya taron lakcar.

Yemi Osinbajo yace gwamnati za ta cigaba da amfani da fasaha wajen sanya ido da yakar ta’addanci kamar yadda ya kamata.

A nasa jawabin, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya tunatar da yadda Sardauna ya shugabanci Arewa baki dayanta kamar yadda ya kamata duk da girmanta.

Kazalika, Mai Alfarma Sarkin Musulmai, Alhaji Sa’ad Abubakar, yace Sardauna ya yiwa kowa da kowa adalchi a lokacin rayuwarsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: