Yadda yan bindiga suka kashe uba ne da ‘ya’yansa 3 a jihar Ebonyi

0 31

An bayar da rahoton kisan mutane 2 a jiya a wani hari dake da alaka da kwarya-kwaryar yaki tsakanin mutanen Ukawu da na Isinkwo a yankin karamar hukumar Onicha ta jihar Ebonyi.

Fadan wanda ake yi akan rikicin kasa ya jawo mutuwar gomman mutane cikin shekara.

An kuma lalata gidaje da dama da sauran kayayyaki a kowane bangare.

Mutane hudun da aka kashe sun fito ne daga kauyen Ukawu.

Wani mazaunin Ukawu yace mazauna kauyen sun yi gabar teku a yankin domin dibar kasa lokacin da ‘yan bindiga suka yi musu kwantan bauna tare da harbe hudu daga cikinsu har lahira.

Mutumin, wanda ya nemi a sakaye sunansa, yace daya daga cikin wadanda aka kashe uba ne da ‘ya’yansa 3, karaminsu watansa 9 a duniya.

Mai magana da yawun ‘yansanda a jihar, Loveth Odah, yace har yanzu rundunar bata samu bayani ba dangane da lamarin.

Amma shugaban karamar hukumar, Felix Igboke, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: