Mutumin da ake jin na daga cikin wadanda suka fi tsufa a duniya ya mutu kasa da wata daya ya cika shekara 113.

Saturnino Garcia wanda tsohon shushana ne ya fito daga birnin Leon na Sfaniya.

An haife shi a shekarar 1909, kuma ya so ya wakilci kasarsa a yaƙin basasar Sfaniya amma tsawonsa bai kai ba.

Da aka tambaye shi sirrin tsawon ransa sai Mr Garcia ya ce “baya shiga gonar da ba tasa ba, kuma baya cutar da mutane.”

BBCHausa

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: