Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya ce gwamnatin tarayya na shirin bunkasa tattalin arzikin Najeriya zuwa darajar dala tiriliyan daya a cikin shekara goma masu zuwa.
Domin cimma wannan buri, Mataimakin Shugaban ya ce ana bukatar aiwatar da manufofi nagari, hadin kai mai ɗorewa, da kuma amfani da basira da hangen nesan kwararru a fannin tattalin arziki.
Shettima ya bayyana haka ne a birnin Legas yayin taron shekarar 2025 na Kungiyar Cibiyoyin Ajiya da Tsabtace Hanyoyin Kasuwanci na Afirka da Gabas ta Tsakiya (AMEDA).
An shirya taron ne tare da hadin gwiwar AMEDA da Kamfanin Central Securities Clearing System (CSCS) Plc, karkashin jigon da ke cewa: “Gina Makomar Kasuwanci: Ginshikan Kasuwancin Kudi a Matsayin Tushen Canjin Tattalin Arziki.”
A jawabinsa, Shettima ya jaddada kudirin gwamnati na karfafa tsarin hada-hadar kudade a Najeriya, ta hanyar hadin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu, da kuma bin tsari na gyare-gyare, tsari mai kyau na kasuwannin hannayen jari, da kafa sabbin dokoki don karfafa ci gaban tattalin arziki.