Gwamnatin tarayya ta amince da kudi sama da N134.7Bn a matsayin kudaden alawus na tsaro

0 185

Ministan tsaro Mohammed Badaru yace gwamnatin tarayya ta amince da kudi sama da naira biliyan 134.7 a matsayin kudaden alawus na tsaro ga manyan hafsoshin tsaro.

Yace amincewar tayi nuni da kokarin gwamnatin na bunkasa walwalar jami’ai, ya kara da cewa wannan din kudade ne da ake warewa domin walwalar jami’ai wanda ya kamata a bayar tun watan junairun daya gabata.

Badaru ya bayyana haka ne yayin da yake karin haske domin bikin ranar tinawa da gudunmawar sojoji a jiya juma’a. Ya ce gwamnatin tarayya zata horar da jami’ai tare da basu kayan aiki na zamani a yunkurin da ake na cigaba da fatattakar yan bindiga.

Leave a Reply

%d bloggers like this: