An kubutar da mutane 8 da akayi yunkurin yin safara a Dutse babban birnin jihar Jigawa

0 415

Hakumar lura da shige da fice ta kasa ta kubutar da mutane 8 da kayi yunkurin yin safara a Dutse babban birnin jiha.

Shugaban hakumar na jiha Samson Umar Agada ya bayyana haka yayin holan wadanda abin ya shafa a shalkwatar rundunar dake Dutse.

A cewar sa, wadanda abin ya shafa sun hada Mata 6 da maza 2 yan tsakanin shekaru 16 zuwa 24 daga jihohin Abia, Benuwai, da Ebonyi.

Ya kara da cewa, an kama wadanda ake zargin ne a tasar mota da Dutse, yayin da wadanda ake zargin anyi safarar suka sanar da jami’ai cewa an shigo da ba bisa ka’aida ba.

Shugaban rundunar na jiha yayi nuni da cewa lokacin da ake gudanar da bincike sun gano cewa, ana safarar su ne domin aiki a wani kamfani dake kan iyaka da jihar Jigawa da Jamhuriyar Nijer zuwa arewacin Afrika.

Yace wadanda aka yi safarar sun hada Friday Amo, Mary Godwin, Barnabas Agatta Chikwado, Gar Godwin da Antonia Nyior.

Sauran sun hada Victoria Amor, Nyior Rita, Barnabas Agape Uchechi da Emeka John.

Samson Agada yace iyayen wadanda abin ya shafa sun tuntubi rundunar amma sun ce ba tare da yardarm su ko amincewar su ake kokarin aikata laifin ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: