Hadaddiyar daular larabawa UAE ta bayyana shirin ta na hadin guiwa da gwamnatin tarayyar Najeriya

0 247

Hadaddiyar daular larabawa UAE ta bayyana shirin ta na hadin guiwa da gwamnatin tarayyar Najeriya domin magance kalubalen ayyukan jin kai da talauci a kasa.

Jakadan na UEA a Najeriya Salem Saeed Al Shamsi ya bada wannan tabbace lokacin da tawagar ofishin jakadancin UAE da gidauniyar Noor Dubai suka kai ziyara ofishin ma’aikatar ayyukan jin kai da yaki da talauci a Abuja.

Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai da hulda  da jama’a na ministar Rasheed Olanrewaju Zubair ya bayyana.

Tawagar ta bayyana dangantar Najeriya da UAE a matsayin mai karfi, tace Hadaddiyar daular larabawa zata yi hadin guiwar ne da Najeriya a fannonin Ayyukan jin kai, samar da ayyuka, abinci mai gina jiki, kiwon lafiya da yaki da talauci.

Da take mayar da jawabi ministar harkokin jin kai da yaki da talauci Dr Betta Edu ta godewa gwamnatin daular larabawa bisa yunkurin su na tallafawa Kasar a dai-dai lokacin da ake bukatar tallafin.

Ministar musamman ta godewa jakadan da tawagar sa bisa ziyarar, tare da bayyana goyon bayansu ta kowace hanya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: