Gwamnatin Tarayya ta ayyana Juma’a a matsayin ranar hutu domin Ranar Dimokuraɗiyya

0 168

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana ranar Juma’a a matsayin hutu na ƙasa, domin tunawa da cikar Najeriya shekaru 27 a jere tana gudanar da mulkin dimokuraɗiyya ba tare da katsewa ba.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis a Abuja, wadda Magdalene Ajani, ta sanya wa hannu a madadin Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida.

A cewar sanarwar, Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hutun a madadin gwamnatin tarayya.

Ya bayyana cewa wannan rana tana da muhimmanci sosai a tarihin Najeriya, kasancewar tana tunatar da al’ummar ƙasar gwagwarmayar da aka yi wajen tabbatar da mulkin dimokuraɗiyya.

Ministan ya kuma jaddada cewa gwamnati na ci gaba da jajircewa wajen kare tsarin dimokuraɗiyya, bin doka da oda, gaskiya, da kuma shugabanci mai inganci da haɗin kai.

Ya ce zaman lafiya da tsaro su ne ginshiƙan ci gaban dimokuraɗiyya da tattalin arzikin ƙasa, don haka gwamnati za ta ci gaba da ɗaukar matakan tabbatar da tsaro a faɗin ƙasar.

A nasa jawabin, ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi amfani da wannan rana wajen yin tunani kan halin ƙasa da kuma gudummawar da kowanne ɗan ƙasa zai bayar wajen inganta dimokuraɗiyya.

Ya kuma tunatar da cewa ranar 12 ga Yuni na daga cikin muhimman ranaku a tarihin Najeriya, domin girmama jarumtar waɗanda suka yi gwagwarmayar kawo dimokuraɗiyya a ƙasar.

A ƙarshe, ya ce gudummawar waɗannan mutane ta ci gaba da zama ginshiƙi wajen tafiyar da ƙasar Najeriya har zuwa yau.

Leave a Reply