Gwamnatin tarayya ta bayyana damuwar ta bisa sace fasinjojin jirgin kasa da aka yi a tashar jirgin kasa ta jihar Edo

0 110

Gwamnatin tarayya ta bayyana sace fasinjojin jirgin kasa da aka samu  a tashar jirgin kasar Tom Ikimi, dake Igueben a jihar Edo a matsayin wani mummunan yanayi da za’a dauki mataki cikin gaggawa.

Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar sufuri Henshaw Ogubike ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa jiya a Abuja.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya rawaito cewa, Igueben hedkwatar karamar hukumar Igueben mahaifar Tom Ikimi ne tsohon ministan harkokin wajen kasar.

A ranar Asabar ne rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta tabbatar da faruwar harin a tashar jirgin kasa da ke jihar.

A cewar rundunar ‘yan sandan, matafiyan suna jiran su hau jirgin kasa daga tashar Igueben zuwa Warri ta jihar Delta ne labarin ya faru.

Ana kuma zargin Yan fashin dajin dayin garkuwa da fasinjojin a yammacin ranar Asabar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: