Ministar Matasa, Jamila Ibrahim, ta ce gwamnatin tarayya ta daina tura mambobin hukumar yi wa kasa hidima, NYSC, zuwa jihohin da ba su da tsaro.
Da take magana a lokacin da take maida martani game da sace wasu masu hidimtawa kasa da aka yi a lokacin da suke yi wa kasa hidima na wajibi na shekara daya, Jamila Ibrahim ta ce shirin ya dauki matakin hana faruwar hakan nan gaba.
Ministar wanda ta bayyana hakan yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi.
A cewarta, tsaron lafiyar masu yiwa kasa hidima na bukatar hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaron gwamnati.
Ministan ta kara da cewa gwamnatin tarayya na kokarin gyara tsarin NYSC dai-dai halin da al’umma ke ciki a halin yanzu, musamman a bangaren alawus-alawus da ake ba su.