Majalisar dattijai na duba yiwuwar sake duba kudaden da hakumar kwastam ke samarwa

0 107

Majalisar dattijai na duba yiwuwar sake duba kudaden da hakumar kwastam ke samarwa na naira biliyan 5.079 daga rabin shekara domin ceto kasar daga ci gaba da  neman rance daga kasashe da hakumomin duniya.

Shugaban kwamitin majalisar dattijai mai kula da hakumar kwastam Isah Jibrin ya bayyana haka a wata ganawa da shugaban hukumar kwastam Adewale Adeniyi da manyan jami’an hukumar.

Sanata Jibrin ya jaddada dalilin da ya sa dole hukumomin su samar da kudaden shigar don inganta tattalin arziki. Da yake amsa tambayoyi daga ‘yan majalisar, shugaban hakumar ta kwastam, ya ce hukumar tana neman amincewar gwamnati domin a sahale musu damar bawa masu motocin da aka yi fasa-kwaurinsu dama su rika biyan kudaden su cikin kasa da watanni 3.

Leave a Reply

%d bloggers like this: