Gwamnatin tarayya ta gargaɗi ‘yan kasuwar da ke da ɗabi’ar ɓoye kayan abinci

0 186

Gwamnatin tarayya ta gargaɗi ‘yan kasuwar da ke da ɗabi’ar ɓoye kayan abinci a daidai lokacin da talakawa ke cikin matsin rayuwa.

Ministan yaɗa labaran ƙasar Muhammad Idris ne ya bayyana haka jim-kaɗan bayan taron gaggawa kan halin matsin rayuwa da tsadar abinci da ‘yan ƙasar ke ciki.

Ministan ya ce gwamnati a nata ɓangare za ta fito da metri ton dubu 42 na abinci daga rumbunan ma’aikatar aikin gona.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake cikin matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa da ake fuskanta a cikin makonnin baya-bayan nan.

Ya ƙara da cewa gwamnati ta ji labarin cewa masu kamfanonin sarrafa shinkafa faɗin ƙasa na da tarin shinkafar da suka taskance, don haka gwamnati ta yi magan da su sun kuma amince za su fito da metric ton 60,000, don a sayar wa ‘yan ƙasar.

Ministan ya ce idan ta kama ma ƙasar za ta ya shigo da abinci daga ƙasashen wajen do magance matsalar tsadar abincin a faɗin ƙasar.

Ministan ya kuma gargaɗi masu ɓoye kayan abinci da su buɗe shagunansu domin mutane su samu damar saya. Yana me cewa duk ɗan kasuwar da ya ki bin wanan umarni to gwamnati ta san su ta kuma san matakin da za ta ɗauka a kansu

Leave a Reply

%d bloggers like this: