Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Wani Tsarin Kiwon Lafiya Ta Hanyar Intanet

0 78

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani tsarin kiwon lafiya ta hanyar intanet wanda zai iya ajiyewa Najeriya dala biliyan 1 da miliyan 200 da ake kashewa a duk shekara wajen tafiya ganin likitoci a kasashen waje.
Da yake kaddamar da dandalin na intanet jiya a Abuja, Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na dijital, Isa Ali Pantami, ya ce asibitin na intanet zai yi amfani da fasahohin da za su inganta harkokin kiwon lafiya a fadin kasar nan.
Ministan ya ce al’adar tafiya ganin likitoci a kasashen waje inda mafiya arziki cikin ‘yan Najeriya ke tafiya zuwa kasashen waje domin samun ingantaccen kiwon lafiya, ana fatan zai ragu sosai ta hanyar wannan tsarin kiwon lafiya na intanet.
Isa Pantami ya nakalto wani rahoto dake cewa karancin likitoci ga adadin marasa lafiya a Najeriya na kara tabarbarewa, inda likita daya ke kula da marasa lafiya sama da dubu 5.
Hakan, a cewarsa, yana sabawa shawarar Hukumar Lafiya ta Duniya WHO sosai wacce tace kamata yayi likita 1 ya duba marasa lafiya 600.

Leave a Reply

%d bloggers like this: