Sama Da Mutane Dubu 40 Ne Ke Mutuwa Kowace Shekara

0 69

Hukumar kiyaye hadurra ta tarayya ta ce sama da mutane dubu 40 ne ke mutuwa a duk shekara sakamakon hadarurrukan ababen hawa a kan tituna a Najeriya.
Shugaban hukumar na kasa, Dauda Biu ne ya bayyana haka jiya a Abuja, yayin da ake gudanar da bukukuwan makon kiyaye hadurra na Majalisar Dinkin Duniya karo na 7.
Ya ce wadannan alkaluman su ne kididdiga marasa dadi na hadurran ababen hawa da kuma jikkatar da ke haddasa mutuwa da nakasa.
Ya kuma ce a duniya mutane miliyan 1 da dubu 300 ke mutuwa yayin da mutane miliyan 50 ke samun raunuka a kowace shekara.
A cewarsa, babu wata barazana ga mutane masu shekaru 5-29 sama da hatsarin motoci, domin daya daga cikin mutane hudun da ke mutuwa suna tsakanin masu tafiya a kafa da kuma masu tafiya akan keke.
Shugaban hukumar ya ce Majalisar Dinkin Duniya ta tsara wani daftarin kasashen duniya na shekaru goma na ayyukan kiyaye hadurra daga shekarar 2021 zuwa 2030.

Leave a Reply

%d bloggers like this: