ZABEN TURKIYYA: Shugaba Recep Tayyip Da Kuma Babban Abokin Hamayyarsa Sun Amince A Je Zagaye Na Biyu

0 63

A yayin da aka kusan kammala kirga dukkan kuri’u da aka kada a zaɓen shugaban kasar Turkiyya shugaba Recep Tayyip Erdogan da kuma babban abokin hamayyarsa sun amince a je zagaye na biyu idan bukatar hakan ta kama.

Alkaluma dai sun nuna cewa Erdogan bai samu kashi hamsin cikin dari da ake bukata ko wani ɗan takara ya samu ba.

Shugaban ya faɗa wa magoya bayansa a birnin Ankara cewa zai sake zama shugaban kasa nan da makwanni 2 kuma ya godewa magoya bayan nasa da suka fito suka zabi son ransu ta hanyar jefa kuri’u ga wanda ya kwanta musu a rai.

Shi kuwa babban abokin hamayyarsa Kemal Kilicdaroglu yana da kashi 45 cikin dari kuma shi ma yayiwa magoya bayansa jawabi, inda ya zargi jam’iyya mai mulki da yunkurin yin kafar ungulu ka kirgen kuri’u.

Ya ce mutanen nan na kokari su kawo tsaiko wajen kirga kuri’u ta hanyar hana ruwa gudu a yankunan da suke da karfi. Kemal dai ya samu goyon bayan matasa da dama da kuma Turkawa, kuma ya ce zai samu nasara idan anje zagaye na biyu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: