Babban Kwamandan Sojojin Sudan Ya Bayar Da Umarnin Kulle Asusun Ajiyar Kudi Na Shugaban RSF

0 73

Babban kwamandan sojojin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan ya bayar da umarnin kulle asusun ajiyar kudi na shugaban tawagar kungiyar RSF da dukkan masu alaka da su.

Cikin wadanda ake zargin suna da alaka da kungiyar RSF da aka bayyana jiya lahdi har da janar Al-Burhan da sauran manyan jami’an soji 4.

Daya daga cikin wadanda hakuncin ya shafa har da brigediya Janar Muhammad Hmadan Dagalo wanda shike jagorantar tagawar dake sasanton zaman lafiya da dakarun sojin kasar a birnin Jidda na Saudiyya.

Janar Burhan ya kuma kori gwamnan babban bankin kasar Hussain Yahia Jankol ya kuma maye wajen sa da E-Saddik.

Koda yake bai bayar da dalilin korar Jankol.

A wani cigaban kuma gidan talabijin mallakin gwamnatin Sudan ya dawo aiki jiya bayan daina yada shirye-shirye na tsawon mako guda. Gidan talabijin din ya daina yada shirye-shirye a mafi yawan lokuta tun bayan soma rikicin a ranar 15 ga watan Afrilu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: