An Shigar Kararraki 17 Dangane Da Zaben Gwamnoni Da Na ‘Yan Majalissu A Jihar Sokoto

0 83

A yau Litinin ne kotun sauraron kararrakin zabe ta 2 ta majalisar dokokin jihar Sokoto za ta fara zamanta na farko kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Sakataren kotun, Sunday Martins ne ya bayar da sanarwar, ya kuma ce an shirya taron kaddamar da kotun 6 da ke harabar babbar kotun jihar Sokoto.

Wadanda ake sa ran a taron na farko akwai babban mai shari’a na jiha kuma kwamishinan shari’a; Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa; Daraktan Sashen Ayyuka na Jiha, Kwamishinan ‘yan sanda; da kuma shugabannin jam’iyyar APC da na jam’iyyar PDP na jihohin.

A kidaya na karshe dai kotun ta samu kararraki 17 dangane da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar tarayya da aka gudanar a ranar 18 ga Maris, 2023, ciki har da na gwamna daya da na ‘yan majalisar wakilai 16, daga ‘yan takara daban-daban na APC da PDP.

Yayin da jam’iyyar APC ta kai karar kujerun majalisar wakilai 10 a Shagari, Sokoto ta Arewa, Tureta, Bodinga ta Arewa, Tambuwal gabas, Gada, Silame, Goronyo, Isa, da Tambuwal yamma, jam’iyyar PDP ta shigar da karar takarar gwamna guda 6 da kuma majalisar wakilai a mazabar Sokoto ta Kudu II, Sabon Birni ta Arewa, Sabon Birni ta Kudu, Binji, Kebbe, da Kware.

Leave a Reply

%d bloggers like this: