Wani Matashi Ya Kashe Mahaifiyarsa Saboda Ta Ki Bashi Kudin Siyan Miyagun Kwayoyi

0 74

Wani matashi mai matsakaicin shekaru mai suna Owate Bode ya kashe mahaifiyarsa a garin Eleme da ke jihar Ribas saboda ta ki ba shi kudin sayan miyagun kwayoyi.

Majiyoyin al’umma sun shaida wa manema labarai cewa, wanda ake zargin wanda aka ce yana shaye-shayen miyagun kwayoyi ya tunkari mahaifiyar tasa inda ya nemi naira dubu 10 da zai saya.

 Majiyar ta kara da cewa kin amincewar mahaifiyar ya jawo masa fushi wanda ya yi amfani da gatari ya sari marigayiyr a kai wanda ta mutu a nan take.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ribas, Grace Iringe Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin. Ta ce wanda ake zargin yana hannun ‘yan sanda kuma ya amsa laifinsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: