Wasu Da Ake Kyautata Zaton ‘Yan Bindiga Ne Sun Kai Hari A Kauyen Fugge Da Ke Jihar Neja

0 81

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kai hari a kauyen Fugge da ke karamar hukumar Rijau a jihar Neja, inda suka yi garkuwa da hakimin kauyen, Malam Abdullahi Zaure da wasu mutane 49.

Wani dan unguwar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce akasarin wadanda aka sace a harin na ranar Juma’ar da ta gabata mata ne, da kananan yara, yayin da kadan daga cikinsu maza ne.

Baya ga wadanda aka sace, an kuma yi awon gaba da shanu da dama.

An tattaro cewa ‘yan ta’addan sun mamaye kauyen ne a kan babura da dama inda suka fara harbin iska don tsorata mutanen kauyen da rana tsaka.

Kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun ya ci tura saboda layin wayarsa bai shiga ba.

A cikin wani sakon da aka aika masa, Abiodun ya yi alkawarin yin bincike tare da bayar da cikakkun bayanai.

Sai dai kakakin ‘yan sandan ya kasa yin hakan har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto. ‘Yan bindiga dai na ci gaba da addabar jihar Neja da sauran jihohin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya duk da kokarin da hukumomin tsaro da gwamnatin tarayya ke yi na shawo kan matsalar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: