Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirinta na soma jigilar dawo da ’yan Najeriya gida da suka makale a kasar Ukraine

0 99

Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirinta na soma jigilar dawo da ’yan Najeriya gida da suka makale a kasar Ukraine da ke fuskantar hare-hare daga dakarun sojin Rasha. 

Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama ne ya bayyana hakan bayan wata ganawa da wakilan ma’aikatarsa suka yi a jiya da Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila.

A wani sako da Ofishin Kakakin Majalisar ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce gwamnatin tarayya za ta fara aikin dawo da ’yan kasarta gida Najeriya daga gobe Laraba.

Ministan ya ce Najeriya ta kammala duk wasu shirye-shiryen dawo da ’yan kasarta gida wadanda suka makale a wasu kasashen saboda yakin Rasha da Ukraine.

Sawaba ta ruwaito cewa tun da farko dai Gwamnatin Tarayya ta sanar da aniyarta na soma dawo da ’yan Najeriya gida daga kasar Ukraine biyo bayan mamayar da Rasha ta yi wa kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: