Gwamnan jihar Sokoto ya sake bude kasuwannin mako-mako da aka rufe a sakamakon hare-haren ‘yan bindiga

0 53

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya sake bude kasuwannin mako-mako da aka rufe a fadin jihar sakamakon hare-haren ‘yan bindiga.

Aminu Tambuwal a ziyarar da ya kai domin raba kayan agaji ga ‘yan gudun hijira a karamar hukumar Tangaza, ya ce matakin ya biyo bayan cigaban da aka samu na tsaro a yankunan da lamarin ya shafa.

Gwamnan Tambuwal ya dakatar da sayar da shanu a kasuwanni, hana kasuwannin mako-mako da kuma sayar da man fetur a jarkoki a wani mataki na dakile rashin tsaro.

Aminu Tambuwal ya ce matakan da gwamnatin jihar ta dauka sun samar da sakamako mai kyau.

Ya ce sakamakon matakan da aka dauka a yanzu ya sa an bude kasuwanni domin mutane su ci gaba da sana’ar saye da sayarwa.

A wata sanarwa da mai magana da yawun sa Muhammad Bello ya fitar a yau, Aminu Tambuwal ya kuma kara nanata cewa har yanzu dokar haramta ayyukan ‘Yan Sakai na cigaba da aiki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: