Dakarun kasar Rasha sun kai hari kan wata hasumiyar gidajen talabijin da ke Kyiv a kasar Ukraine

0 36

Mai bayar da shawara ga ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar Ukraine, Anton Herashchenko, ya ce dakarun kasar Rasha sun kai hari kan wata hasumiyar gidajen talabijin da ke Kyiv.

Gidan talabijin na Channel 1+1, ya ce za a yi aiki don maido da hanyar sadarwar da ta dauke.

Wata kafar yada labarai ta kasar Ukraine mai amfani da harshen Ingilishi da ke da hedkwata a babban birnin kasar, ta ce tashoshin talabijin na Ukraine sun daina yada labarai bayan harin.

A halin da ake ciki kuma, mai bayar da shawara ga ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar Ukraine ya ce mutane 10 ne suka mutu, yayin da wasu 35 suka jikkata, sakamakon harin rokoki da sojojin Rasha suka kai a tsakiyar birnin Kharkiv, birni na biyu mafi girma a Ukraine.

Hakan na zuwa ne bayan da akalla mutane 11 suka mutu a jiya sakamakon wani harin roka da Rasha ta kai kan birnin na Kharkiv.

Babu wani martani daga Rasha game da daya daga cikin labaran yayin da Al Jazeera ta kasa tantance sahihancin su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: