Yan Najeriya 400 na jihohi 7 za su ci gajiyar shirin samar da ayyukan yi na Hukumar Samar da Ayyukan yi ta kasa a bangaren sana’o’in hannu

0 95

Kimanin ‘yan Najeriya 400 ne a jihohi bakwai da babban birnin tarayya za su ci gajiyar shirin samar da ayyukan yi na hukumar samar da ayyukan yi ta kasa (NDE) a bangaren sana’o’in hannu.

A cewar sanarwar da mataimakin daraktan yada labarai da hulda da jama’a na hukumar, Edmund Onwuliri, ya fitar kuma aka rabawa manema labarai a Abuja, jihoshin sun hada da Jigawa, Kogi, Rivers, Edo, Kaduna, Ebonyi da Kebbi.

A wani labarin kuma, Cibiyar Bayar da Agaji ta Sarki Salman ta kasar Saudiyya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da gidan agaji na Abubakr As-Sidiq domin raba kwandunan abinci dubu 2 da 300 ga gidaje a Najeriya a cikin watan Ramadan mai zuwa.

Wakilan Cibiyar Bayar da Agaji ta Sarki Salman da kuma gidan agaji na Abubakr As-Sidiq a Abuja ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a karshen mako.

Aikin rabon agajin zai ciyar da musulmin Najeriya masu fama da matsanancin talauci su dubu 12 da 600.

Leave a Reply

%d bloggers like this: