Ministan ilimi ya sha alwashin gwamnati na ganin ta magance matsalolinsu ASUU

0 69

Biyo bayan barazanar da suka yi na cigaba da zanga-zangar sai baba ta gani, ministan ilimi, Malam Adamu Adamu, a jiya da daddare ya gana da daliban da suka gudanar da zanga-zangar, inda ya sha alwashin gwamnati na ganin ta magance matsalolinsu.

Ministan wanda tun da farko ya fice daga wajen ganawa da daliban a jiya da safe kan abin da ya bayyana a matsayin rashin kirkin shugabannin daliban, daga bisani ya gana da shugabannin kungiyar dalibai ta kasa (NANS) a hedikwatar hukumar kula da jami’o’i ta kasa.

Ya kuma tabbatarwa masu zanga-zangar cewa ‘yan kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da suke yajin aikin za su koma aiki nan ba da jimawa ba.

A cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na ma’aikatar, Ben Goong, ya fitar a daren jiya, ministan ya ce shirin tattaunawar da ake yi ya samu sakamako mai kyau kuma ana sa ran zai kai ga gaggauta dawo da malaman da suke yajin aiki zuwa bakin aiki.

Sai dai daraktan bai bayar da cikakken bayanin ganawar ministan da shugabannin daliban ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: