Majalisar Dattawa ta zartar da kudirin bayar da cikakken ikon cin gashin kai na kudade da na mulki ga kananan hukumomi

0 112

Majalisar Dattawa ta zartar da kudirin bayar da cikakken ikon cin gashin kai na kudade da na mulki ga kananan hukumomi.

Kudirin dai na neman yin gyara ga kundin tsarin mulkin kasa domin soke asusun hadin gwiwa na kananan hukumomi da jihohi tare da samar da asusu na musamman inda za a biya duk wani kason kananan hukumomin, daga asusun tarayya da na jiha.

A cikin kudirin kudirin, kowace karamar hukuma za ta kirkiri tare da kula da asusunta na musamman da za a kira da suna asusun rabo na kananan hukumomi, wanda za ake saka dukkan kason karamar hukumar a cikinsa.

Dokar ta kuma umurci kowace jiha ta biya kananan hukumomin da ke yankinta kudaden shigar da take samu a cikin wadannan sharuddan da kuma yadda majalisar ta tsara.

Domin samun ‘yancin cin gashin kai ta fuskar mulki, kudirin na neman baiwa kananan hukumomi damar gudanar da zabukansu da kan su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: