‘Ko matasa sun san ni matashi ne’ – Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

0 104

Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana kansa a matsayin matashi.

Bola Tinubu ya yi wannan tsokaci ne a daidai lokacin da ake ta ce-ce-ku-ce kan matasa su karbi mulki.

A yayin da yake tabbatar da cewa yana da karfin da zai jagoranci kasar nan, Tinubu ya ce yana da ikon yi wa Najeriya hidima da kuma daukaka kasarnan.

Ya shaida wa magoya bayan sa a wajen wani taro na baya-bayan nan cewa jam’iyyar APC za ta ci gaba da kare muradun ‘yan Nijeriya na gida da waje.

Gabanin zaben 2023, matasan Najeriya na ta tada jijiyoyin wuya kan cewa matashi ya karbi mulki daga hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Da yake jawabi a lokacin da ya ziyarci wani Sarkin a Kudu maso Yamma a farkon watannan, Bola Tinubu ya ce yana son matashi ya zama shugaban Najeriya, amma hakan zai faru bayan ya zama shugaban kasa.

An haife shi a ranar 26 ga Maris 1952, Bola Tinubu zai yi bikin cika shekaru 70 a duniya nan da ‘yan makonni.

Leave a Reply

%d bloggers like this: