Yadda wasu ‘yan bindiga suka yi awon gaba da wasu sabbin amare a jihar Neja

0 101

Wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wasu sabbin amare a karamar hukumar Lavun da ke jihar Neja a karshen mako.

An rawaito cewa ‘yan bindigar da suka fara kai samame kimanin kauyuka 10 a ranar Asabar a karamar hukumar, sun dawo da safiyar jiya.

A lokacin da suka dawo, rahotanni sun ce mutane da yawa sun tsere daga gidajensu sakamakon harin da aka kai a ranar da ta gabata.

Wani dan uwa ga amaren da aka sace, Yakubu Mohammed, ya tabbatar da cewa an tafi da amaren a lokacin da aka kai harin.

A cewar mazauna yankin, maharan da suka yi yunkurin guduwa da shanun da suka sace zuwa kauyen Akare da ke karamar hukumar Wushishi ta jihar sun gama da iftila’in rugujewar wata gada.

Kwamishinan kananan hukumomi, masarautu, ci gaban al’umma da tsaron cikin gida na jihar Neja, Emmanuel Umar, ya tabbatar da aukuwar harin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: