Gwamnatin Tarayya ta ware Naira miliyan dubu 600 da za ta bayar a matsayin bashi domin tallafawa manoma miliyan 2 da dubu 400

0 118

Gwamnatin Tarayya a karkashin shirin inganta rayuwa da habaka aikin gona ta ware kudi naira miliyan dubu 600 da za ta bayar a matsayin bashi domin tallafawa manoma miliyan 2 da dubu 400 a fadin kasarnan.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sanar da haka jiya a Abuja a wajen bikin bude baje kolin kayan aikin gona na kasa domin ranar abinci ta duniya ta bana.

Shugaba Buhari, wanda ya samu wakilcin ministan aikon gona da raya karkara, Mohammed Abubakar, yace za a bayar da bashin ba tare da kudin ruwa ba.

A nasa bangaren, shugaban kwamitin aikin gona na majalisar dattawa, Sanata Abdullahi Adamu, yace gwamnatin Shugaba Buhari ta kirkiri shirye-shirye da kudirori akan cigaban aikin gona da yalwar abinci a kasarnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: