Gwamna Ganduje ya nemi a yi sulhu

0 99

Abdullahi Umar Ganduje, yayi kira ga ‘yan Najeriya da su rungumi tattaunawa, girmamawa da fahimtar juna domin dakile rashin jituwar dake tsakaninsu, inda yace kasarnan ta yi dadewar da bai kamata ake tunanin raba ta ba.

Gwamna Ganduje ya bayar da shawarar a jiya a wajen taron ‘yan asalin Arewa maso Yamma domin hadin kan kasa, zaman lafiya da tsaro, wanda cibiyar hulda da jama’a ta kasa ta shirya a Kano.

Gwamnan, wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Alhaji, yace taken taron ya bayyana halin da ake ciki a halin yanzu a kasarnan, inda yace kaunarsa ga hadin kasa ya sanya ya baya kowa da kowa damar zama a Kano a matsayin dan asalin jihar.

Shima da yake jawabi, Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Umar Namadi, yace duk kokarin da gwamnati da hukumomin tsaro suka yi da nufin dakile rashin tsaro, dole ne sai ‘yan kasa sun bayar da hadin kai kafin a samu maslaha.

Leave a Reply

%d bloggers like this: