Shugaba Buhari ya nemi agajin shirin cigaba na Majalisar Dinkin Duniya wajen sake tsugunnar da ‘yan gudun hijira a Arewa maso Gabas

0 76

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a jiya ya nemi agajin shirin cigaba na majalisar dinkin duniya wajen sake tsugunnar da ‘yan gudun hijira a Arewa maso Gabas.

Yayi magana a fadar shugaban kasa da ke Abuja lokacin da ya karbi bakuncin shugabar shirin cigaba na majalisar dinkin duniya, shiyyar Afirka, Ahunna Eziakonwa.

Shugaba Buhari yace shirin cigaba na majalisar dinkin duniya ya cancanci yabo saboda tallafin da ya bawa Najeriya zuwa yanzu, a bangarori daban-daban, musamman wajen samar da zaman lafiya a Arewa maso Gabas.

Yace gwamnati na yin iya bakin kokarinta wajen sake tsugunnar da ‘yan gudun hijira a gidajensu, amma yayi nuni da cewa da kudade kalilan, kuma za ayi maraba da tallafin hukumomi irinsu shirin zaman lafiya na majalisar dinkin duniya.

Ya godewa Ahunna Eziakonwa wacce ‘yar Najeriya ce bisa ziyarar da ta kawo, inda yayi nuni da cewa da ita da Ngozi Okonjo-Iweala ta hukumar cinikayya ta duniya da Amina Mohammed, mataimakiyar sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, suna fitar da Najeriya kunya a idon duniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: