Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kudi naira miliyan dubu 1 da miliyan 400 ga ma’aikatar ilimi

0 42

Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kudi naira miliyan dubu 1 da miliyan 400 cikin watanni hudun da suka gabata ga ma’aikatar ilimi, kimiyya da fasaha, domin ginawa da gyaran makarantun firamare da kananan sakandare a fadin jihar.

Kwamishinan ma’aikatar ilimi, kimiyya da fasaha na jiha, Dr. Lawan Yunusa Danzomo, wanda ya sanar da haka a jiya, yayin taron manema labarai a cibiyar horas da ma’aikata ta Manpower dake Dutse, yace an kashe wasu daga cikin kudaden wajen gina azuzuwa da samar da kayan koyo da koyarwa tare da gyaran wasu makarantun da suka lalace.

Dangane da ilimin bai daya, kwamishinan yace gwamnatin jihar ta samu nasarar samar da kujeru da kayan koyo da koyarwa a makarantun gaba da firamare.

Ya kuma sanar da kafa ajujuwan koyar da Fulani makiyaya domin basu ilimin addini da na boko.

Leave a Reply

%d bloggers like this: