Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya sake fatali da amincewar da majalisar dattawa ta yi a wani kudirin dokar gyara zabe

0 81

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya yi fatali da amincewar da majalisar dattawa ta yi a wani kudirin dokar gyara zabe wanda ya bayar da umarnin gudanar da zaben kato bayan kato domin zaben ‘yan takarar da jam’iyyun siyasa za su tsayar.

Sule Lamido, wanda dan Jam’iyyar PDP ne, ya ce umarnin ya sabawa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya kuma ya shawarci jam’iyyarsa ta kalubalanci matakin a kotu.

Majalisar dattawa, a ranar Talata, ta amince da sashin bayan ta canja matsayinta na farko don yin yarjejeniya tare da Majalisar Wakilai kan tsayar da ‘yan takarkarun jam’iyyu a zabe.

A wata sanarwa da ya fitar jiya, Sule Lamido ya ce Kundin Tsarin Mulki ya bai wa jam’iyyun siyasa damar tsara yadda ake gudanar da al’amuransu kuma ya umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta tabbatar sun bi ka’idojin kundin tsarin mulkinsu.

Sule Lamido ya ce majalisar kasa, wacce ke karkashin ikon jam’iyyar APC, ta mayar da kanta a matsayin mai kula da jam’iyyun siyasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: