Gwamnatin tarayya tace ta cimma matsaya da kungiyar kwadago ta TUC

0 336

Gwamnatin tarayya tace ta cimma matsaya da kungiyar kwadago ta TUC, na tsawon makonni biyu domin magance matsalar kungiyar.

Wannan na zuwa ne bayan fara yajin aikin gargadi na kwanaki biyu wanda kungiyar kwadago ta NLC ta fara a jiya.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar kwadago da ayyukan yi Olajide Oshundu ya fitar.

Ya bayyana cewa, ganawar da shugabannin kungiyar kwadago suka yi da Ministan kwadago, an samu nasara a cikin ta,inda dukkan bangarorin biyu suka cimma yarjejeniya domin baiwa gwamnati damar biyawa kungiyar bukatun ta cikin makonnin 2.

Tunda farko shugaban kungiyar TUC ta masu masana’antu Festus Osifo, ya tabbatar da cewa Mambobin kungiyar su basa cikin wannan yajin aikin.

A wani batun kuma shugaban kungiyar kwadago ta NLC Joe Ajaero ya yabawa da bin umarnin da suka bayar da zama a gida.

Inda ya bukaci Mambobin kungiyar a dukkan matakai da suka ci gaba da zama a gida tun daga jiya zuwa Laraba 6 ga wannan wata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: