Gwamnatin Tarayya tace zata kai shirin ciyar da daliban makaranta zuwa mataki na gaba

0 82

Gwamnatin Tarayya tace zata kai shirin ciyar da daliban makaranta zuwa mataki na gaba.

Ministar jin kai, kula da annoba da walwalar jama’a, Sadiya Umar Farouq, ta sanar da haka cikin wata sanarwa da mai taimaka mata ta musamman akan sadarawa, Halima Oyelade, ta fitar yau a Abuja.

Sadiya Farouq tace ma’aikatarta tare da tallafin fasaha daga shirin abinci na majalisar dinkin duniya, zasu inganta shirin na ciyar da daliban makaranta domin magance yunwa tsakankanin yara kanana.

Ta bayyana cewa sabon matakin zai bunkasa tattalin arzikin cikin kasa tare da karan yawan yaran da ake sakawa a makaranta da yawaitar zuwa makaranta akai-akai daga daliban makarantun firamare.

Ministar ta bayyana cewa zuwa shekarar da ta gabata, shirin ya ciyar da dalibai sama da miliyan tara a makarantun firamaren gwamnati guda dubu 53.

Leave a Reply

%d bloggers like this: