Hukumar NITDA ta fara shirin horas da masu sana’o’in hannu da matasa akan ilimin komfuta da gyaran wayoyin hannu

0 70

Hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa (NITDA) ta fara shirin horas da masu sana’o’in hannu da matasa akan ilimin komfuta da gyaran wayoyin hannu.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar a Abuja ta hannun shugabar sashen yada labarai na hukumar, Hadiza Umar, kuma aka bawa kamfanin dillancin labarai na kasa.

Sanarwar tace aikin horon, wanda aka fara a jiya, zai habaka ilimin komfuta da samar da sana’o’i ga matasan Najeriya tare da ilimomin da ake bukata wajen samar da sana’o’i.

Sanarwar ta kuma ce an shirya bayar da horon ne da nufin dakile tulin matsalolin dake fuskantar kasarnan musamman karancin ilimin sana’o’i tsakankanin dumbin matasan da basu da aikin yi.

Sanarwar ta kara da cewa za a gudanar da aikin bayar da horon a jihoshi 4 na Gombe, Kogi, Neja da Oyo.

Leave a Reply

%d bloggers like this: