

- Wasu ‘yan bindiga sun kashe wakilai uku na ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar PDP daga karamar hukumar Mariga ta jihar Neja - May 26, 2022
- Dalilan da yasa wasu ‘yan takarar gwamna 2 na jam’iyyar APC suka yi watsi da zaman ganawar da gwamna Badaru ya kira domin a samar da dan takarar daya tal - May 26, 2022
- Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da aka dakatar, Abba Kyari ya garzaya wata babbar kotun tarayya domin neman belinsa - May 26, 2022
Hukumar yaki da cuta mai karya garkuwa jiki ta jihar Jigawa JISACA tace ta yiwa ma’aurata dubu 350 gwajin cutar kafin su yi aure a bara.
Manajan shirye shirye na hukumar Ibrahim Almajiri ya sanar da hakan ta cikin wani shirin Radio Jigawa.
Yace hukumar ta gudanar da gwajin ne ga maza da mata da za su yi aure daga ciki da kuma wajen jihar Jigawa.
Yace hukumar ta ware cibiyoyin lafiya guda 21 domin yin gwajin ga al’umma a kyauta da nufin gano ko suna dauke da cutar ko kuma akasin hakan.
Ibrahim Almajiri ya kara da cewar hukumar tana bayar da maganin cutar kyauta ga masu dauke da cutar tare da tallafawa masu cutar da suke san yin aure.
Ya bukaci al’umma dasu tabbatar an musu gwajin cutar domin sanin matsayinsu, inda yace akwai dokar hukumar da ta hana tsangwamar masu dauke da cutar a fadin jiharnan.