

Hukumar yaƙi da cin hanci a Najeriya EFCC ta gurfanar da shahararren mai amfani da shafukan zumunta, Ismaila Mustapha da aka fi sani da Mompha, a kotu.
Cikin waɗanda EFCC ta gurfanar har da kamfaninsa mai suna Ismalob Global Investment Limited.
An gurfanar da su ne a gaban Mai Shari’a Mojisola Dada na Kotun Laifuka na Musamman da ke Jihar Legas.
Ana tuhumar su da laifi takwas da suka ƙunshi zamba da kuma halsta kuɗin haram.