Gwamnatin Tarayya tana hasashen samun kudaden shiga na naira tiriliyan 10 da biliyan 700 a bana

0 92

Gwamnatin Tarayya tana hasashen samun kudaden shiga na naira tiriliyan 10 da biliyan 700 a bana.

Ministar kudi, Zainab Ahmed, ta sanar da haka a jiya a wajen bayanin sassan kudirin kasafin kudin bana ga jama’a da aka gudanar a Abuja.

Tace adadin ya haura hasashen bara na naira tiriliyan 8 da biliyan 100 da kashi 32 cikin 100.

Kamar yadda yazo a kudirin kasafin kudin, za a kashe tirilyan 8 da biliyan 600 wajen rage basussuka.

Ta cigaba da bayyana cewa kasafin kudin bana yana da gibin naira tiriliyan 6 da biliyan 300 kuma za a cike giben ta hanyar ciyo sabbin basussuka daga cikin kasa da kasashen waje da Hukumomi da kuma kudaden da za a samun idan aka sayar da kadarorin gwamnati.

Ana sa ran ciyo bashin naira tiriliyan 2 da rabi daga cikin kasa, kuma a ciyo wata tiriliyan 2 da rabin daga kasashen waje. Kazalika za a ciyo bashin naira tiriliyan 1 da biliyan 100 daga hukumomi, sannan a samu naira biliyan 90 daga kudaden sayar da kadarorin gwamnati.

Leave a Reply

%d bloggers like this: