Wata gobara tayi sanadiyyar mutuwar wani yaro dan shekara 4 tare da kone gidaje hudu da lalata dukiya ta miliyoyin naira a nan jihar Jigawa.

Lamarin ya auku ranar Litinin da dare a garin Mabab dake mazabar Batu a yankin karamar hukumar Birniwa ta jiharnan.

Shugaban Karamar hukumar, Alhaji Umar Baffa Birniwa, ya tabbatar da lamarin bayan ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan wanda ya rasu.

Umar Baffa yace ba a san musabbabin gobarar ba.

Yace an kashe gobarar bisa kokarin hukumomin tsaro da masu agaji.

Yayi addu’ar Allah ya jikan wanda ya rasu tare da alkawarin tallafawa wadanda gobarar ta shafa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: