Shugaba Buhari ya ce ya ayyana yan bindiga a matsayin yan ta’adda

0 100

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta ayyana ’yan bindigar da suka addabi yankin Arewa maso Yammacin Najeriya a matsayin ’yan ta’adda.

Ya ce jami’an tsaro za su fara daukar su a haka sannan su yi maganinsu.

Matsayin dai na zuwa ne bayan da aka shafe tsawon lokaci ana kiran gwamnatin ta yi haka.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels a ranar Laraba.

A cewarsa, gwamnatinsa ta yi nasara wajen yaki da matsalar tsaro musamman a Arewa maso Gabashin kasar nan, yankin da Boko Haram da mayakan ISWAP suka fi addaba.

Shugaban, ya ce lokacin da ya karbi mulki a 2015 wasu daga cikin kananan hukumomi na karkashin ikon Boko Haram, wanda a yanzu ba haka abun yake ba.

Sai dai ya ce a yanzu babu wata Karamar hukuma da ke karkashin ikon ’yan ta’addan.

Da yake karin haske kan matsalar tsaro a yankin Arewa maso Yamma kuwa, ya ce an samu ci gaba musamman a mako shida da suma gabata, bayan zaman tattaunawa da ya yi da manyan shugabannin tsaron kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: