Gwamnatin tarayya bata da wani kuduri na rage yawan ma’aikatan gwamanati a Najeriya – Ministar kudi

0 63

Ministar kudi, kasafi da tsare-tsare Zainab Ahmed Shamsuna, tace gwamnatin tarayya bata da wani kuduri na rage yawan ma’aikatan gwamanati a fadin kasar nan.

Zainab Shamsuna ta bayyan haka ne a cikin shirin barka da Safiya na gidan talabijin na kasa NTA da safiyar yau alhamis.

Ministar ta musanta rade-radin da ke yawo cewa gwamanati na shirin korar ma’aikata daga aiki domin rage barnatar kudade.

Tace shugaban kasa Buhari ya nanata cewa baza’a kori kowa ba, haka kuma ministan tace gwamnati tana bawa mutane Kwarin guiwar tsayawa da kafarsu maimakon Dogara da aikin gwamnati, ta hanyar basu basussuka da tallafi.

Zainab Shamsuna tace gwamnati taza rage kashe kudade domin cimma burukan da aka sanya agaba da kuma cigaba da tafiya da sauran hakumomi a kasar nan.

Kazalika tace shugaban kasa ba shida burin ragewa maaikata lokacin aiki, wanda ake bashi shawara tun farkon hawansa kugerar mulkin kasar nan.

Haka kuma ministar tayi tawassali da cewa shugaba Muhammadu buhari bai taba kin biyan albashi, ko fansho ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: