Gwamnatin Tarayya za ta dauki tsauraran matakai a kan likitocin da suka shiga yajin aiki, Dokta Chris Ngige

0 61

Ministan Kwadago da Ayyuka Dokta Chris Ngige, ya ce Gwamnatin Tarayya za ta dauki tsauraran matakai a kan likitocin da suka shiga yajin aiki.

Tun ranar Litinin likitocin suka fara yajin aiki bisa zargin Gwamnatin Tarayya da kin mutunta yarjejeniyar da ta kulla da su.

Biyo bayan kokarin da gwamnatin tarayya da ma’aikatarsa na sukayi na ganin likitocin sun janye yajin aikin ya ci tura.

Dr Ngige ya ce yajin aikin da Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta Kasa (NARD) ta shiga ‘shirme’ ne, don haka ya sa ’ya’yansa wanda suke aikin likita su kaurace masa.

Ministan ya sha alwashin daukar tsattsauran mataki a kan likitoci matukar ba su koma bakin aikinsu ba, kamar yadda ya shaida wa gidan talabijin na Channels a jiya Juma’a da dare.

Ya ba wa likitocin nan da mako mai zuwa su koma bakin aikinsu, idan ba haka ba gwamnati za ta dauki matakin babu aiki, babu biyan albashi.

Ministan ya ce saboda muhimmancinsu ga al’umma, bai kamata su fara yajin aiki ba, ba tare da sun sanar dashi kwana 15 kafin ranar ba.

Kazalika, Dr Christ Ngige ya zargi gwamnatoci jihohi, bisa yadda suke yiwa lamarin rikon sakainar kashi, inda ya ce gwamnatin tarayya tana mayar da hankalin ta ne kan huruminta kadai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: