Za a taimakawa tubabbun tsagerun Neja Delta dan su dogara da kansu

0 49

Kwamitin Shugaban Kasa kan yi wa tubabbun tsagerun Neja Delta afuwa ya yi kira gare su da su tsara sabbin dabarun kasuwanci don a taimaka musu su zama masu dogaro da kansu.

Shugaban riko na kwamitin, Kanal Milland Dixon Dikio (mai ritaya) shine ya yi kiran lokacin da yake jawabi ga rukunin farko na wadanda shirin ya shafa da aka zabo daga jihohin Akwa Ibom da Kuros Riba a karshen mako.

Kakakin shugaban, Mista Nneotaobase Egbe cikin wata sanarwa a yau Asabar ya ce manufar shirin ba wai kawai su ci gaba da dogaro da N65,000 din da ake basu a kowanne wata ba ne, sai don su zama suna daukar nauyin wasu.

Mista Dikio ya ce, karfafa musu gwiwa su rubuto tsare-tsaren kasuwancinku don a taimaka muku ku dogara da kanku, tare da shirya musu bitocin kasuwanci don koya musu ingantattun hanyoyin samu kudi kuma na halal. Kazalika ya ce akwai damammaki iri-iri ba wai kawai biyan kudi ba, inda ya kara da cewa a matsayinsu na wadanda abin ya shafa, ya kamata su yi amfani da su wajen bunkasa yankinmu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: