Fulani makiyaya sun koka bisa yin biris da umarnin gwamnatin jihar Jigawa ga wayanda suka cinye makiyaya da mashaya

0 48

Fulani Makiyaya na garin Ayyan Fulani na karamar hukumar Auyo, sun koka bisa abinda suka kira yin biris da umarnin da gwamnatin jihar Jigawa ta bada mahukuntan kananan hukumomin da suka cinye Makiyaya da Mashaya su dawo musu da wuraren su cikin gaggawa.

Fulanin sun bayyana kukan nasu ne a lokacin da suka kawo mana ziyara a nan gidan Radiyo Sawaba.

Shugaban Fulani Malam Ibrahim Ayyan Fulani ya ce har yanzu suna cigaba da bibiyar gwamnati kan umarnin da ta bayar ga kananan hukumomin da suka cinye makiyaya da Mashaya su mayarwa Fulani.

A watan daya gabata ne Kwamishinan Ma’aikatar Kasa da Safiyo Hon Sagir Musa Ahmed, ya fitar da wata sanarwa, inda yake umartar Mahukuntan kananan hukumomi su dawowa da Fulani wuraren da suka karbe daga hannun su, kuma suka sayarwa Mutane.

Zamu cigaba da bibiyar wannan labari har zuwa wani lokaci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: