Kungiyar Tsoffin Daliban Makarantar Hudu Model Qur’an sun bada tallafin kayan Makaranta

0 102

Kungiyar Tsoffin Daliban Makarantar Hudu Model Qur’an Yan Ajin shekarar 2012, sun bada tallafin kayan Makaranta (Uniform a turance) ga Dalibai 10 wanda Iyayen su suke da karamin karfi domin tallafa musu.

Da yake jawabi a lokacin mika kayan, a madadin mambobin kungiyar, Shugaban Kungiyar Nasiru Hamza Abdullahi, ya ce kungiyar ta yanke shawarar aiwatar da hakan ne domin tallafawa Dalibai 10 daga cikin daliban da suke Makarantar kuma Iyayen su suke da karamin karfi wajen Dinka musu kayan makaranta.

A cewarsa, daliban da suka ci gajiyar shirin sun kunshi Maza da Mata, inda ya kara da cewa tallafawa daliban makarantar, dama sauran dalibai, yana daga cikin kudurin kungiyar.

A jawabinsa, shugaban Makarantar ta Hudu Model Qur’an Malam Muhammad Haruna, ya godewa mambobin kungiyar bisa bada tallafin, inda yayi kira da sauran daliban Makarantar suyi koyi da abinda na gaba dasu sukayi.

Wasu daga cikin daliban da suka amfana da tallafin sun bayyana farin cikinsu, tare da godewa mambobin kungiyar bisa basu tallafin kayan makaranta kyauta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: