Yadda wani matashi dan shekara 25 ya rataye kansa a kyauyen Chamo na karamar hukumar Dutse

0 67

Rundunar yan Sandan Jihar Jigawa ta bayyana cewa wani Matashi dan shekara 25 mai suna Nura Muhammad, ya rataye kansa a kyauyen Chamo na karamar hukumar Dutse.

Kakakin Rundunar na jihar Jigawa ASP Lawan Shiisu Adam, shine ya tabbatar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN a Dutse.

A cewarsa, mutumin wanda yake zaune a kyauyen Chamo, ya rataye kansa ne da misalin karfe 12:30 na Rana a dakin sa.

ASP Lawan Shiisu Adam, ya ce tun da farko mutumin ya fadawa matarsa cewa, akwai yuwuwar mutuwarsa a nan gaba.

Kakakin rundunar yan sandan ya ce Matar marigayin, ta fadawa yan sanda cewa mijin nata yana fama da tabuwar hankali, tun bayan daya dawo daga jihar Lagos a watan Yuli.

Kazalika ya ce bayan faruwar lamarin ne aka dauki gawar mutumin, zuwa babban Asibitin Dutse, domin yin gwaje-gwaje, inda likita ya tabbatar da musuwarsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: