Wasu barayi sun kashe wani matashi mai achaba a karamar hukumar Birnin Kudu

0 102

Rundunar Yan Sandan Jihar Jigawa ta bayyana cewa wasu da ake kyautata zaton barayi ne sun kashe wani Matashi Mai Sana’ar Achaba, dan shekara 23 a karamar hukumar Birninkudu ta jihar nan.

Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar yan Sanda ta Jiha ASP Lawan Shiisu Adam, shine ya tabbatar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN dake Dutse.

ASP Lawan Shiisu Adam, ya ce Marigayin mai suna Umar Abubakar dan kyauyen Lautai dake karamar hukumar Birninkudu, an tsinceshi ne a jiya Juma’a da misalin karfe 8:20 na Safe.

Haka kuma ya ce barayin ne suka kashe Matashin, ta hanyar shakeshi, inda kuma suka tafi da Babur din nasa.

Kakakin rundunar ya ce bayan sun halarci wurin ne, suka dauki gawar Matashin zuwa Asibiti, inda aka tabbatar da mutuwar tasa.

Kazalika, ya ce rundunar tana cigaba da farautar mutanen da ake zargi da kashe mutumin domin gurfanar dasu a gaban Kuliya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: