Kungiyar Gwamnonin Jam’iyar PDP ta bukaci mambobi da sauran Masu ruwa da tsaki na Jam’iyar su kai zuciya nesa

0 65

Kungiyar Gwamnonin Jam’iyar PDP ta bukaci mambobi da sauran Masu ruwa da tsaki na Jam’iyar su kai zuciya nesa, biyo bayan musabus din da wasu Jagororin Jam’iyar 7 sukayi.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jam’iyar PDP, kuma Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya fitar a Abuja.

Gwamna Tambuwal, ya bukaci mambobin Jam’iyar su kasance masu hakuri, da son zaman lafiya, a daidai lokacin da mambobin Jam’iyar suke kokarin shiga lamarin domin sasantawa.

A cewarsa, kungiyar ta damu da halin da Jam’iyar PDP take ciki, na rikicin cikin gida, inda ya kara da cewa kungiyar ta kira taron gaggawa domin tattaunawa da nufin samun mafita.

Haka kuma ya ce Jam’iyar PDP ita kadai ce mafita ga yan Najeriya, biyo bayan yadda Jam’iyar APC ta kasa magance matsalolin yan Najeriya.

Kimanin Jagororin Jam’iyar PDP 7 ne sukayi murabus, daga mukaminsu na Majalisar Zartarwa na Jam’iyar, biyo bayan abinda suka kira rashin iya shugabancin Prince Uche Secondus, shugaban Jam’iyar na Kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: